Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi ta sanya sabon wa’adin rijistar maniyyata aikin hajjin shekarar 2025.
An kayyade wa’adin yin rajistar ne a ranar 5 ga Fabrairu, 2025, kamar yadda gyare-gyaren da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta yi.
Hakan ya fito ne a wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Alhaji Faruk Aliyu Yaro, Jagaban Gwandu, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, kuma aka bayyanawa manema labarai a ranar Talata.
Sanarwar ta ce, gyaran da hukumar ta NAHCON ta yi ya tilastawa hukumomin jin dadin Alhazai da hukumomin jihar da su fitar da duk wani abin da aka tara kafin ranar 1 ga watan Fabrairun 2025, wanda ya sa aka sauya wa’adin rajistar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa sama da kashi 60% na kudin aikin Hajjin bana an riga an fara aiwatar da su tun bayan fara rajistar a watan Satumban 2024, inda ya rage kashi 40% kawai.
Sanarwar ta bukaci maniyyata da su yi amfani da sauran lokacin da suka rage sannan su yi ajiya kafin sabon wa’adin don tabbatar da halartar aikin Hajji mai zuwa.
“Ana bukatar maniyyata da su yi ajiyar kudi har miliyan takwas, Naira dubu dari hudu (N8,400,000.00) ta hanyar daftarin banki daga kowane bankin kasuwanci, wanda za a biya ga hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi.”
“Za a gudanar da rijistar ne a kan hanyar da ta dace, tare da bin ka’idar yin adalci wajen bayar da hidima.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, maniyyatan da a baya suka yi ajiya amma ba su iya zuwa aikin Hajjin da suka gabata ba, dole ne su cika kudadensu don samun mafi karancin ajiya kafin wa’adin ranar 5 ga watan Fabrairu don samun kujerunsu.
Daga nan ya bayyana kudirin hukumar na inganta ayyuka ga maniyyatan da suka yi rajista, tare da yin alkawarin cewa za a aiwatar da sabbin dabarun inganta aikin Hajji baki daya.


