An sanya wa wasu jarirai biyu da aka haifa a cikin Ukraine sunayen wasu rokokin yaki na Birtaniya.
Wasu kafofin yada labarai na Ukraine ke cewa, Jariran biyu namiji da mace ne, kuma an sanya wa namijin Yan Javelin, ita macen kuma an sanya ma ta Javelina.
An yi rajistar wadannan sunayen ne a Vinnytsia Oblast kamar yadda matar tsohon shugaban Ukraine Kateryna Yushchenko ta sanar.
Kateryna ta ce, alama ce ta yabon da ‘yan Ukraine ke wa kasashen Yammacin Turai, saboda makaman da suke tura wa kasar.