fidelitybank

An sanya ranar da za a yanke wa Matashin da ya ƙona Masallata a Kano hukunci

Date:

Wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta karanta wa Shafi’u Abubakar matashin da ake zargi da cinna wa mutane wuta a masallaci tuhume-tuhume guda huɗu da ake yi masa waɗanda suka haɗa da;

Zargin sanadiyyar kisan mutum 23 da gangan ta hanyar cinna musu wuta a masallaci a garin Gadan wanda aka fi sani da Larabar Abasawa cikin ƙaramar hukumar Gezawa.

Yunƙurin kisan wasu mutum biyu a ranar 15 ga watan Mayu 2024 a garin Gadan.

Raunata wasu mutane ta hanyar watsa musu fetur a masallaci lamarin da ya yi sanadin haifar musu da munanan raunika.

Ƙone masallaci da abubuwan da suke ciki alƙalin kotun Ustaz Halhalatul-khuza’i Zakaria ya tambayi Shafi’u Abubakar wanda ake tuhuma ko ya fahimci tuhumar sai ya amsa da cewa “E” ya fahimta tare da tabbatar da cewa “lalle haka abin yake ya aikata”.

Babbar kotun Shari’ar Musuluncin ta ɗage zamanta zuwa ranar 1 da 2 ga watan gobe na Agustar 2024, inda ake fatan kotun za ta yi masa hukuncin kamar yadda masu kara suka nema.

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp