Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu Imam Ogan Boye, ya ce ƙaramar hukumar za ta ɗauki matakan gaggawa kan lalacewar maƙabartu musamman a wannan lokacin damina.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na ƙaramar hukumar Nassarawa, Sharif Zahraddeen Usman Kofar Nassarawa, ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Agusta, 2025.
Shugaban ya ce sama da makabartu 25 aka gano suna bukatar cike ramuka saboda ruftawar ƙasa da ruwan sama ya jawo.
Ya kuma bayyana yiwuwar samar da babura ga masu sintirin dare domin inganta tsaro a makabartu.
Ya ƙara da cewa makabartu za su kasance wurin da za a kiyaye mutunci da darajar al’umma, saboda haka ƙaramar hukumar za ta ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa sake faruwar irin wannan matsala.