Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanya dokar hana fita ta s’o’i 24 a unguwannin Sabon Garin Nassarawa da Tirkaniya a yankin ƙaramar hukumar Chikun.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne bayan wani rikici na ‘yan sara-suka da ya kaure, da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.
Sanarwar ta kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar da dokar a unguwar, domin maido da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin abin da ya haddasa hargitsin.
Domin haka ne kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su yi biyayya ga dokar hana fitar, wadda ta fara aiki nan take.