Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta Tarayya ta sanar da ‘yan Najeriya game da barkewar cutar anthrax a jihar Zamfara.
Daraktan sashen yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Ben Bem Goong, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ci gaban ya bukaci a kara sanya ido da kuma daukar matakai don dakile hadurran da ke tattare da cutar.
Ya ce, “Anthrax, wanda kwayoyin cuta, bacillus anthracis ke haifarwa, cuta ce ta zoonotic da za ta iya shafar dabbobi daban-daban masu dumin jini kamar shanu, tumaki, awaki, dawakai, da namun daji, da kuma mutane.”
Daraktan ya bayyana cewa cutar anthrax an sanya shi a matsayin cutar da Hukumar Kula da Lafiyar Dabbobi ta Duniya, WOAH ta bayyana, saboda yadda yake iya haifar da cututtuka da kuma mace-mace.
A cikin dabbobi da kuma mutane, ya bayyana cewa alamun cutar anthrax sun hada da zazzabi, tari, amai, tashin zuciya, gudawa, ciwon makogwaro da kumburin lymph nodes, ciwon kai, ƙaiƙayi da zubar jini daga manyan wuraren buɗe ido.
Goong ya kuma shawarci manoman dabbobi da su samar da matakan kariya, yana mai tabbatar da cewa ana iya yin rigakafin cutar ta Anthrax ta hanyar hada kai kamar tantance hadarin, bincike da kuma allurar zobe na dabbobi masu saurin kamuwa da su a wuraren da ke da hadari, gano gaggawa da kuma mayar da martani na da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwar ta.
“Dangane da barkewar cutar, ma’aikatar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki, musamman jihohin da ke kan iyaka da Zamfara, da su dauki matakin gaggawa don hana ci gaba da yaduwar cutar,” in ji shi.
Ma’aikatar ta bukaci jama’a da su kasance cikin taka tsantsan, da bayar da rahoton duk wata cuta da ba a saba gani ba a cikin dabbobi ko mutane, tare da bin duk ka’idojin kariya daga hukumomin da abin ya shafa.