Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne ya bayar da karin haske kan binciken da ake yi wa marigayi mawakin, Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad.
Owohunwa ya bayyana cewa ‘yan sandan sun gano jimillar shaidu 26.
CP ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da bayani kan mutuwar mawakin.
Ya kuma bayyana cewa an yi wa mutane biyar tambayoyi.
“Ya zuwa yanzu an gano shaidu 26 a binciken da ake yi na Mohbad.
“Ya zuwa yanzu an yi wa mutane biyar tambayoyi game da binciken da ake yi,” in ji shi.