fidelitybank

An samu sauyin tashin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja

Date:

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya, ta sanar da sauya lokutan tashin jiragenta guda biyu daga tashar Idu zuwa Rigasa.

Manajan sufurin jiragen kasan, mista Pascal Nnorli, shi ya tabbatar da hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai ta Najeriya, NAN a yau Juma’a.

Mista Pascal ya ce daga yanzu jirgin kasa da ke tashi 3:30 daga tashar Idu a Abuja, zai koma tashiwa 3:00, inda kuma zai isa Kaduna 5:08 na yamma.

”Sannan Jirgin da ke tashi 2:00 na rana daga tashar Rigasa, a yanzu zai koma tashiwa 1:30 na rana, ya kuma isa Abuja 3:37 maimakon 4:07 na yamma.” in ji mista Pascal.

Ya ce sauyin zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Disamban da muke ciki.

Mista Nnorli, ya kuma ce hukumar kula da jiragen kasan na yin duk mai yiwuwa domin kare lafiya da dukiyoyin fasinjojinta a kowane lokaci.

Kamfanin sufurin jiragen kasan ya dawo zirga-zirga ne a ranar 5 ga watan Disamba bayan kusan wata takwas da kai wa wani jirgi hari a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maÆ™ale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi É—an shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin Æ´an Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taÉ“a barin Iran ta Æ™era makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaÆ™i – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...
X whatsapp