Mahukuntan Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti (EKSU) da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun samu rarrabuwar kawuna kan yadda ake dawo da harkokin ilimi a makarantar.
Jami’ar a ranar Litinin ta umurci dalibai da ma’aikata da su koma ranar 24 ga Mayu, 2022 don ci gaba da zaman karatu na zangon 2020/2021.
Sai dai kungiyar ASUU a jami’ar, ta nesanta kanta daga komawar da kungiyar ta sanar, inda ta dage cewa, malaman na cikin yajin aikin da kungiyar ta kasa ta kaddamar a fadin kasar.
Kungiyar, a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar, Dakta Kayode Arogundade da sakataren kungiyar, Dakta Olawale Ogunwale, suka sanyawa hannu, ta umarci mambobin kungiyar da su yi watsi da sanarwar komawa aiki, inda suka bukaci su bi umarnin kungiyar ASUU ta kasa baki daya sabanin sanarwar da cibiyar ta fitar. A cewar The Nation.