Rahotonni daga jihar Kano na cewa an ga wasu da ake zargin wakilan wasu jam’iyyun siyasa ne na raba atamfa da yaduka har ma da kuɗi.
Hotuna da BBC ta samu sun nuna yadda mutane suke karɓar irin waɗannan atamfofi, yayin da wasu kuma suka ƙi karɓa.
Karanta Wannan: Gwamnan Bauchi ya jefa kuri’arsa
Jihar Kano dai na ɗaya daga cikin jihohin da ake ganin zaɓen gwamna zai yi zafi sosai tsakanin ‘yan takara.