Dan wasan Juventus Paul Pogba, an tabbatar da gwajin ƙwayoyin ƙara kuzari, bayan wasan da suka yi da Udinese a Seria A, in ji Corriere della Sera.
Rahoton ya ce Pogba yana da kwanaki uku don amsa tuhumar da ake masa.
Hanya ce ta al’ada ga ‘yan wasa su yi gwajin maganin kara kuzari nan da nan bayan wasa a mafi yawan fitattun kungiyoyin Turai.
Pogba ya buga karawar da Bologna da Empoli kafin a yi zargin an tabbatar da gwajin nasa don kula da kwayoyin testosterone.
Yanzu dole ne tsohon dan wasan tsakiyar Manchester United ya gabatar da tantance sakamakon.
Idan aka samu Pogba da laifi, haramcin yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a Seria A na iya daukar matakin dakatarwa daga buga wasa na tsawon shekaru biyu zuwa hudu, wanda zai bar dan wasan mai shekaru 30 cikin babbar matsala.


