fidelitybank

An samu matsala tsakanin Dubai da Najeriya ta bangaren Biza

Date:

Hukumar shige da fice ta kasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa ‘yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A wata sanarwa da suka aike wa kamfanonin shirya tafiye-tafiye a Najeriya ranar Juma’a, hukumomin kasar ta UAE sun ce ”duka takardun neman izinin biza da aka cike an dakatar da su yanzu”.

Jaridar The Cable a Najeriya ta ruwaito gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duka wadanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.

Ta kuma ce ”kin amincewar ya shafi kowanne dan Najeriya, dan haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu”.

Ta kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba ne zuwa lokacin da za ta sulhunta da gwamnatin Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne wata guda bayan da kasar ta UAE ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga ‘yan kasa da shekara 40, lamarin da ya shafi ‘yan Najeriya da na wasu kasashen.

Ko a shekarar 2021 ma dai ƙasashen biyu sun shafe watanni masu yawa suna ce-ce-ku-ce game da harkar sufurin jiragen sama.

nnnhausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp