Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u a zaɓen gwamnoni a jihohi 28 da na ƴan majalisar dokokin jihohi da aka gudanar a ranar Asabar.
An samu rahotannin tayar da hargitsi a yankuna daban-daban lokacin zaɓen.
A wani yanki na jihar Legas, wasu sun yi yunƙurin satar akwatin zaɓe, sai dai ba su samu nasara ba, inda aka bi su aka ƙwace akwatin.
An samu rahotannin kai farmaki kan rumfunan zaɓe a Sokoto da Kano da kuma Port Harcort.
Sai dai da alama na’urar BVAS ta yi aiki fiye da lokacin zaɓen shugaban ƙasa, inda bayanai ke cewa an samu nasarar tura sakamako ta na’urar a wurare da dama