An samu barazanar bam har biyar amma na ƙarya a wuraren kaɗa ƙuri’a a gundumar Fulton da ke jihar Georgia a safiyar yau.
Nadine Williams, shugabar sashen rajista da zabe na gundumar, ta ce barazanar ta kai ga kwashe mutane na wucin gadi a wasu wurare biyu na kusan mintuna 30.
A halin yanzu mahukunta a yankin, wanda ya haɗa da birnin Atlanta, suna aiki don samun umarnin kotu domin tsawaita lokacin zaɓe a wuraren biyu da abin ya shafa har zuwa karfe 00:30 GMT.
Mun ruwaito a baya cewa tangarɗar na’ura a gundumar Cambria ta jihar Pennsylvania ta hana wasu masu kaɗa ƙuri’a tantance kuri’unsu, kuma jami’an zaɓe a jihar sun miƙa buƙatar tsawaita lokacin kaɗa ƙuri’a.