fidelitybank

An samu asarar rayuka 182 a Kano cikin shekarar 2021 – Hukumar kashe gobara

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce sama da kadarori na Naira miliyan 660 ne suka salwanta a gobarar da ta afku a fadin jihar a shekarar 2021.

Jami’in hulda da jama’a na SFS, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai, ya ce an samu kiran kashe gobara 831 daga gidajen kashe gobara 27 a fadin jihar, inda ya ce jami’an hukumar sun kai daukin gaggawar ceto 818.

Abdullahi ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Disamba, 2021, sun samu kira na karya 201.

Ya ce”Mutane 98 ne suka mutu daga jimillar mutane 113 da suka fada cikin tafki ko rafuka yayin da su ke ninkaya, akalla mutane 37 ne suka fada a cikin rijiya kuma daga adadin, 27 da abin ya shafa sun mutu”.

Abdullahi ya yi nuni da cewa, a lokuta daban-daban, an yi asarar rayuka 182 daga watan Janairu zuwa Disamba 2021.

Ya bayyana cewa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar sun ceci kadarorin da ya kai N1, 579,706,274 daga watan Janairu zuwa Disamba, 2021.

A cewarsa, a lokacin damina ta shekarar da ta gabata, an samu rugujewar gini guda biyu, inda aka ceto mutum daya da wutar lantarkin ta kama a gidan titin jirgin na Kofar Nassarawa.

Ya ce, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Hassan Ahmad Muhammad Muhammad ya shawarci jama’a da su kula sosai da kayayyakin wuta domin gujewa tashin gobara.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp