Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ɓullar fari-ɗango a Najeriya, tare da wasu tsuntsaye suma masu illa ga amfanin gona a jihohi uku na arewacin kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya shafi jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara ne.
Shugabar likitocin dabbobi ta kasa, Dr Maimuna Habibu ta ambao cewa, an samu mamayar farin ne a jihohin Zamfara da Kebbi, amma za su iya kutsawa har jihar Sokoto.
A ranar Asabar ta ce, tuni ma’aikatarsu ta aike da jami’ai, domin fara yakar wadannan fari.
Ta ce Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ne biyo bayan korafin da ta samu daga manoma a johohin da abin ya shafa.