Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting ya fitar ya nuna cewa an samu karuwar rashin tsaro a watan Mayun 2024 da kashi 10.28 inda aka samu faruwar al’amura da ke nuna taɓarɓarewar tsaro sau 762, idan aka kwatanta ta watan Afrilun da ya gabata da al.amuran rashin tsaro suka faru sau 691.
” Wattan Mayun 2024 ya gano yadda rashin tsaro ya ƙara ƙamari inda ya ƙaru da kaso 262.70 saboda samun ƙaruwar garkuwa da mutane. Ana kuma alaƙanta hakan ne sakamakon hare-haren ƴan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar….” In ji rahoton.
To sai dai rahoton ya nuna cewa duk da samun ƙarin matsalolin tsaro da aka samu a watan Mayun amma kuma an samu ragin yawan mace-mace a watan inda alƙaluman suka ragu zuwa 1090 daga 1097 a watan Afrilu.
Hakan in ji rahoton na nuna raguwar mace-macen ne da kaso 0.64.
Rahoton ya kuma lissafa jihohin da aka fi samun matsalolin da suka haɗa da Borno da Edo da Abuja da Kaduna da Katsina da Kogi da Kwara da Niger da Sokoto da kuma Zamfara.
Daga ƙarshe rahoton ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ɗauki dukkannin matakan da suka kamata wajen ganin an kare dukiya da rayukan al’umma.