Kwararru a fannin kiwon lafoya sun ce, an samu karuwar yaduwar cutar kyandar biri a Najeriya, inda yanzu ta bazu zuwa jihohi 26 ciki har da Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Jaridar Daily Trust, wadda ta rawaito wannan labari, ta kara da cewa kwararrun sun ce wannan lamari abin tsoro ne wanda yake bukatar ba shi kulawar da ta dace.
Ana daukar cutar ce daga dabbobi kuma ana yada ta a tsakanin mutane.
Tun daga farkon watan Janairun 2022 zuwa Augustan shekarar, an samu mutum 473 da ake zargi sun kamu da cutar, a in da aka tabbatar mutum 172 da suka kamu da ita a cikinsu.
Bayanan da aka samu daga hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasar, NCDC, sun nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar a 2022 kawo yanzu, ya fi na wanda aka samu a 2017 da 2018 da 2019 da 2020 da kuma na 2021.
Tun daga farkon shekarar 2022, kasashe da dama ke fuskantar bullar cutar ta kyandar biri, abin da ya sa shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Gebreyesus, ya ayyana dokar ta-baci a kanta a ranar 23 ga watan Yulin shekarar.


