An sallami gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, daga asibiti bayan an tabbatar da ya samu sauƙi daga raunin da ya samu sakamakon hatsarin mota a hanyarsa daga Katsina zuwa Daura.
Gwamnan ya samu kulawa ta musamman daga masana lafiya, kuma yanzu an tabbatar da cewa ya dace da komawa bakin aiki ba tare da wata matsala ba.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, likitan da ke kula da lafiyar gwamnan ya tabbatar da cewa ya samu sauƙi sosai, kuma ya shirya tsaf don ci gaba da gudanar da ayyukan mulkinsa.
Bayanin da gwamnatin jihar dai ta fitar game da hatsarin ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da gwamna Radda ke kan hanyarsa ta zuwa Daura, inda wata mota ƙirar Golf ta kauce hanyarta, kuma ta faɗa wa motar da gwamnan ke ciki.