Rahotanni daga jihar Katsina, na cewa an sako ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Dutsin Ma, bayan shafe sama da wata biyu a hannun ‘yan fashin daji.
A ranar Laraba 4 ga watan Oktoba ne, wasu ‘yan bindiga suka auka gidan ɗaliban dukkansu mata, da ke zaune a wajen jami’ar cikin unguwar Maryama Ajiri da tsakar dare.
Hukumomi dai sun ce suna ci gaba da tuntuɓa da tattaunawa don ganin an sako ɗaliban ba tare da wani lahani ba.
Lamarin ya faru ne ƙasa da mako biyu bayan sace wasu ɗalibai ‘yan mata a Jami’ar Tarayya ta Gusau cikin jihar Zamfara mai maƙwabtaka.
Duka jihohin biyu suna fama da rikicin ‘yan fashin daji waɗanda ke kai hari kan garuruwa da ƙauyuka tare da sace mutane don yin garkuwa da su da zimmar neman kuɗin fansa.
Zuwa yanzu dai BBC ba ta samu cikakken bayani a kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sako ɗaliban na Jami’ar Dutsin Ma, ko a’a ba.