An saki ɗalibai da malamai ƴan asalin ƙasar Poland da aka kama a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Poland ya bayyana a ranar Laraba.
Mutum bakwan sun shiga hannu ne a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, “bisa zargin su da hannu a ɗaga tutocin Rasha da ma ita kanta zanga-zangar,” kamar yadda jami’an tsaron Najeriya suka bayyana.
Sai dai hukumomi a ƙasar Poland sun ce waɗanda aka kama ɗin ɗalibai ne na Jami’ar Warsaw da malaminsu, waɗanda “tsautsayi ya kai su inda bai dace ba.”
Ministan Harkokin Wajen Poland, Radoslaw Sikorski ya ce yanzu an sako ɗaliban.
“Ina tabbatar da cewa an sako mutanenmu ɗin nan, yanzu haka sun koma Kano sun ci gaba da karatunsu,” kamar yadda Sikorski ya wallafa wani bidiyo a shafi X.
Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa za su koma ƙasarsu ta Poland bayan sun kammala karatunsu.