Masu garkuwa da mutane sun saki ɗalibin makarantar Bethel Baptist ta Kaduna, bayan shafe fiye da shekara biyu a hannunsu.
A ranar Juma’a ne aka saki Treasure Ayuba, wanda shi ne ɗalibi na ƙarshe da ya rage a hannun masu garkuwa da mutanen, bayan shafe shekara biyu da wata huɗu a hannunsu.
A cikin watan Yulin 2021 ne dai wasu gungun ‘yan bindiga suka dirar wa makarantar ‘Bethel Baptist High School’ da ke ƙauyen Maraban Damishi a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka sace ɗaliban makarantar 121.
Gwamnan jihar sanata Uba sani ya bayyana jin ɗaɗinsa da sako ɗalibin.
Yayin da yake gidayarsa ga ubangiji kan wannan lamari, Gwamnan ya kuma gode wa mutane hukumomi bisa ƙoƙari da addu’o’in da suka yi don tabbatar da kuɓutar da ɗalibin.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke kai samame ƙauyuka da sace mutane don neman kuɗin fansa, da ƙona musu gidaje bayan sace dukiyoyinsu.