fidelitybank

An saki daliban jami’ar Wukari daga hannun ‘yan ta’adda

Date:

Ɗalibai biyu daga jami’ar gwamnatin tarayya ta Wukari da ke jihar Taraba da ake zargin masu garkuwa sun sace su sun shaƙi iskar ƴanci.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an saki ɗaliban ranar Alhamis da daddare a kusa da ƙauyen Chinkai da ke ƙaramar hukumar Wukari.

Shugabar sashen yaɗa labarai na jami’ar, Ashu Agya ce ta bayyana hakan ga Channels ta wayar tarho.

A cewarta an biya kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban.

Tun farko kafar yaɗa labaran ta ruwaito cewa an sace ɗaliban da ƙarfe 10 na dare ranar 1 ga watan Afrilu a wani wajen cin abinci da ke wajen harabar makarantar.

A ranar da lamarin ya faru, masu garkuwar sun yi ƙoƙarin sace wasu ɗaliban sai dai ba su yi nasara ba abin da ya janyo suka lakaɗawa ɗaliban da masu shagon duka tare da sace kayansu.

Kashi 90 cikin 100 na malamai da ɗaliban makarantar na zama ne a wajen jami’ar kamar yadda shugaban jami’ar ya faɗa a bikin yaye ɗalibai da aka yi a baya-bayan nan.

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp