Rahotanni na cewa al’ummar Birnin Gwari na jihar Kaduna da Dugun Mu’azu na ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da wasu yankunan jihar Neja sun sake zama jiya Laraba da ƴan bindigar yankunan domin jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar Kaduna ta cimma.
Waɗanda suka halarci taron sun bayyana cewa ƴanbindigar sun bayyana dalilan da ya sa suka riƙa kai hare-hare duk da yarjejeniyar, inda daga bisani suka nemi yafiya tare da neman a sake bude wasu kasuwannin yankin.
Zubairu Abdulra’uf Ɗanmasanin Birnin Gwari wanda ke cikin waɗanda suka halarci zaman ya yi wa BBC Hausa ƙarin bayani, inda ya ce an sake tattaunawa, sannan an sabunta yarjejeniyar domin ci gaba da zaman lafiya a yankunan.