Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta ce ta sake karɓar ‘yan ƙasar 294 a ranar Litinin da aka kwaso daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar.
Wata sanarwa daga hukumar ta ce jirgi biyu ne ya kwaso mutanen daga garin Agadez na Nijar zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ne da ke Kano bayan sun maƙale a can.
Ta ce jirgin farko ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:30 ɗauke da mutum 148, na biyun kuma ya sauka da mutum 146 da misalin ƙarfe 4:29 na yamma.
Bayanai sun nuna akasarin mutanen kan maƙale ne bayan yin zango a Agadez yayin da suke kan hanyarsu ta kaiwa ƙasashen Aljeriya ko Libya ko kuma nahiyar Turai.
Ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasashen duniya ne ke taimakawa tare da hadin gwiwar gwamnati wajen mayar da su gida a jirgi.