Sojoji ƙarƙashin rundunar kakkaɓe dazuka daga ƴan ta’adda a yankin arewa maso gabas sun kuɓutar da ƙarin ƴar makarantar Chibok, Lydia Smith.
Rahotanni daga jaridun Najeriya na cewa sojojin runduna ta 82 a ƙaramar hukumar Gwoza sun kuɓutar da Lydia ne tare da ƴaƴanta uku a ranar Laraba.
Jaridun sun ruwaito cewa Lydia ta miƙa wuya ga dakarun a Gwoza. Tana ɗauke da juna biyu da ya kai wata biyar kuma ta yi iƙirarin cewa ta fito daga garin Pemi a Chibok.
A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka cika shekara 10 tun bayan da Boko Haram ta sace ƴan matan su 276 daga makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.
57 daga cikin ɗaliban sun kuɓuta byan sace su, 16 kuma an kuɓutar da su daga bisani sai wasu 107 da aka sake su a lokuta daban-daban bayan da aka tattauna.
Gwamnati da sojojin Najeriya sun yi alƙawarin ƙwato ragowar ƴan matan da har yanzu suke hannun mayaƙan na Boko Haram.