Wasu da ake zargin Fulani ne sun sake kai hari tare da kashe mutane kusan bakwai a kauyen Warkan da ke filin Atyap da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Rahotanni na cewa maharan sun kuma kone gidaje da dama, inda kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka jikkata ba.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun afkawa kauyen ne cikin dare a yawansu.
Ya ci gaba da bayyana cewa, “Ba zai iya fahimtar dalilin da ya sa wadannan hare-hare da kashe-kashe da suka zama ruwan dare a Atyap land ba.
“Abin da ya fi daukar hankali shi ne gazawar masu rike da madafun iko, a matakin tarayya da na jihohi wajen daukar kwararan matakai don kawo karshen hare-haren.”