Rasha da Ukraine sun bayyana cewa an kara harba makamai a kusa da tashar sarrafa nukiliya ta Zaporizhzhia.
Bayanai na cewa an harba makaman ne da nufin kai hari a garin Enerhodar mai makwaftaka da tashar, wanda ke hannun dakarun Rasha.
Kamar yadda suka saba, kasashen biyu sun dora wa juna alhakin harin.
Wani injiniya dan kasar Ukraine da ke aiki a tashar ya ce ya ga sojojin Rasha na harba makamai a tashar a baya-bayan nan.
Wakiliyar BBC ta ce ya ce ya shaida yadda dakarun Rasha suka kai hari kan wani bangare na cibiyar daga cikin harabarta.
Ya shaida wa BBC cewa Rasha ta yi kokarin kai hari a kan layukan da ke samar da lantarki ga na’urorin sanyaya na’urorin cibiyar, kuma ya ce idan aka lalata sauran layukan lantarkin to za a iya fadawa cikin bala’in da nukiliyar ka iya haifarwa.


