Kafofin yada labarai na Amurka, sun ce, hadiman Shugaba Joe Biden, sun sake gano karin kunshin wasu takardun bayanan sirri na tun yana mataimakin shugaban kasa.
Tarin takardun farko an gano su ne a wani ofishi da ba na gwamnati ba a Washington, wanda kuma Mista Biden ke amfani da shi.
An ruwaito cewa an gano su ne a wani gini na daban, amma ba a san ainahin wurin ba ko kuma matsayin girman sirrin takardun.’
A ranar Talata Mista Biden ya ce, bai san abin da takardun farkon suka kunsa ba, amma dai yana bayar da hadin kai ga binciken da Ma’aikatar Shari’a ke yi a kai.
Kwamitocin majalisar dokokin kasar masu kula da bayanan sirri sun nemi a yi musu karin haske kan takardun na Biden da kuma, uwa-uba masu yawa wadanda tsohon shugaban kasar Donald Trump ya rike, lokacin da ya bar mulki, wadanda ba a son ransa ba ya mika su.