Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya ta ce ta gano aƙalla gawarwaki 54 a wurin da hatsarin kwale-kwalen jihar Kogi ya auku ranar Juma’ar da ta gabata.
Ana dai kyautata zaton cewa har yanzu ba a ga fiye da mutum 100 ba, yayin da aka ceto wasu 24 da ransu.
Ƙwararrun ninƙaya da masu iyo na ci gaba da neman sauran mutanen, sai dai fatan samun ragowar mutanen da rai na ci gaba da raguwa a zukatan al’umma.
Kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji fiye da 200 ya kife a cikin ruwan Kogin Neja tsakanin jihohin Kogi da Neja da ke tsakiyar Najeriya, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Katcha.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) mai kula da ofishin Kogi Mista Justin Uche ya shaida wa BBC cewa rashin ingantaccen tsari ya sa har yanzu ba a kai ga gano cikakkun bayanai game da fasinjojin ba.
“Matsalar ita ce, babu tsarin adana bayanin fasinjoji, don haka bayar a cikakkun bayanan fasinjojin ke da matuƙar wahala”, in ji Mista Uche.
Gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ya bayar da umarni ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta samar da kayayyakin agaji ga iyalan mutanen da abin ya shafa,” in ji wata sanarwa daga ofishin gwamnan.
Haka kuma gwamnan ya buƙaci asibitocin da aka kwantar da mutanen da aka ceto da rai, su ba su kulawar da ta dace.
Gwamnan na Kogi ya kuma koka kan yadda ake yawan samun haɗurran a harkar sufurin ruwa a Najeriya, sannan ya buƙaci a tsaurara matakan da suka dace don ganin an kauce wa samun irin waɗannan haɗurran a nan gaba.