Hukumar da ke Kare Muradan Masu Saye ta Kasa, FCCPC ta sake buɗe katafaren kantin sayar da kayayyaki na Sahad Stores, bayan rufe shi.
A ranar Juma’a 16 ga watan Fabrairu ne hukumar ta garƙame babban kantin, saboda zargin yadda ake cuwa-cuwar sanya farashin kayayyaki a kantin.
Hukumar ta yi zargin cewa masu gudanar da katafaren kantin na ƙara wa abokan hulɗarsu kuɗin kaya fiye da farashin da ke maƙale a jikin kayan.
FCCPC ta ce hakan na tilasta wa kwastomomi biyan kuɗaɗe masu tsada don sayen kayayyaki.
To sai dai cikin wata sanarwa da mai riƙon muƙamin mataimakin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi, ya fitar ya ce an sake buɗe kantin domin ci gaba da cinikayya.


