A ranar Asabar da ta gabata ne wasu makiyaya suka harbe wasu makiyaya biyu tare da sace shanu 223 a Haying Dam da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna. ‘Yan bindigar da yawansu ya kai, an ce sun kai hari a sansanonin makiyaya uku da ke yankin da bindigogi kirar AK-47.
Rahotanni na cewa al’amarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata da misalin karfe 6 na yamma, inda ‘yan bindigar suka fara kai hari a sansanin wani Alhaji Ibrahim Yabari tare da yin awon gaba da shanu 123, kafin daga bisani suka wuce sansani na biyu suka kwashe shanu 100. A cewar wata majiya, “daya daga cikin ‘yan fashin ya bude wuta tare da kashe wasu makiyaya biyu a lokacin da suke kokarin hana su satar shanun. Majiyar ta bayyana cewa, dakarun da ke makwaftaka da kauyen Janjala, sun zo wurin al’umma kuma har yanzu suna kan bin sahun ‘yan fashin. Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, bai amsa kiran da aka yi masa a wayar salula ba.