Wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Tudun Doki da ke yankin ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar Sotoko inda suka kashe mutum biyar tare da sace mutanen da ba a san adadinsu ba.
Rahotonni sun ce ‘yan bindigar sun far wa ƙauyen ne da tsakar daren ranar Sallah.
Gwamnatin Jihar ta tabbatar wa BBC faruwa kai harin, inda ta ce an jikkata fiye da mutum 30 a lokacin harin.
Jihar sokoto da ke arewacin ƙasar na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga ke sace mutane masu yawa a lokaci guda domin neman kuɗin fansa.