Dakarun tsaron Iran sun sace gawar wata matashiyar mai zanga-zanga ‘yar shekara 16, inda suka binne ta cikin sirri a wani kauye, cewar majiyoyi na kusa da iyayenta.
Iyayen matashiyar sun shirya binne Nika Shakarami a ranar Litinin, amma sai aka kwace gawarta inda aka binne ta a wani kauye mai nisan kilomita 40 daga mahaifarta.
Nika ta bata tsawon kwana 10 bayan ta shiga cikin masu zanga-zanga a birnin Tehran ranar 20 ga watan Satumba.
Wata ‘yar uwar mahaifiyarta ta fada wa BBC cewa sakon da ta aika wa wata kawarta a karon karshe shi ne wasu jami’an tsaro suna bin su da gudu.
Iyayen Nika daga karshe sun gano gawarta a wani dakin ajiye gawawwaki na wata cibiyar tsare mutane a babban birnin.
Inda suka dauko gawarta zuwa gidansu da ke Khorramabad a yammacin kasar ranar Lahadi.
Bayan an tursasa musu, iyayen matashiyar sun amince su yi mata jana’iza amma sai dakarun tsaro suka “sace” gawar Nika inda suka binne ta a kauyen Veysian in ji daya daga cikin maiyoyin.