fidelitybank

An sace daliban Najeriya fiye da 1,500 – Amnesty

Date:

Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin da Adam ta Amnesty International ta ce shekara takwas bayan da kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan matan makarantar Chibok 276, fiye da dalibai 1,500 wasu kungiyoyi suka sace, kuma hukumomin kasar sun kasa kare su.

Amnesty International ta bayyana haka ne cikin wani rahoton da ta fitar.

Rahoton kungiyar ya ce, a cikin dalibai 276 na Chibok da aka sace, an kashe 16 kuma har yau ba a san inda 109 suke ba.

Sannan a dalilin sace daliban da ake yi an sun kulle makarantu masu yawa kuma an fara yi wa dalibai mata auren wuri.

Amnesty ta kuma ce an sace dalibai 1,500 cikin wata 22 ne, kuma har zuwa wannan lokacin akwai dalibai kimanin 120 da ke hannun wadanda suka sace su.

Cikin dalibai 102 da aka sace a makarantar gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri, har yanzu tara na hannun masu garkuwa da su, haka kuma ba a sako daya daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist High School ta Kaduna cikin dalibai 121 da aka sace ba.

Sannan an kashe dalibai biyar na jami’ar Greenfield ta Kaduna, kuma wani dalibin makarantar sakandaren Kankara ma ya rasa ransa. In ji BBC.

Akwai kuma dalibai biyar na makarantar Islamiyar Salihu Tanko da ke Tegina da masu garkuwa da su suka kashe, inda a karshe rahoton ya bayyana cewa daliba Leah Sharibu ta makarantar gwamnati da ke Dapchi ce kadai ba a sako ba cikin dalibai 276 da aka sace.

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp