Akalla shagunan 50 na sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba aka rufe a jihar Kogi.
Shugaban kungiyar Pharmaceutical Society of Nigeria (PSN), Dr Lawal Muhammed na jihar Kogi ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida, a ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta 2022.
Dakta Muhammed wanda ya koka kan yadda masu shagunan sayar da magunguna na babu da ke yaduwa a jihar Kogi, ya jaddada cewa, idan ba a gaggauta tantance su ba, zai haifar da babban hadari ga tsaro a fadin kasar nan.