Hukumomi a Habasha, sun ce sun rufe otel-otel da mashaya da kuma gidajen rawa da ake zargin ana ayyukan luwaɗi.
Hukumar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta Addis Ababa ta ce tana ɗaukar matakin ne a kan duk wani waje da masu neman jinsi guda suna ayyukan su.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a facebook ta ce an gano wuraren ne bayan samun bayanai daga jama’ar gari a kan ɓata-garin da kuma maɓoyarsu. In ji BBC.
Ta kuma ce za ta ci gaba da kai samame irin wuraren da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Habasha ta haramta luwaɗi, amma a baya-bayan nan ana samun rahotannin ɓullar masu irin wannan ɗabi’a a ƙasar.