Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu goma sha daya a fadin jihar.
Gwamnatin ta ce rufewar ya biyo bayan gano cewa wasu mutane na yin mu’amala da shanu ba tare da cikakkun bayanai ba kamar yadda doka ta tanada.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Mumir Haidar Kaura ya fitar.
Ya kuma kara da cewa, an sanar da rufe kasuwannin sakamakon rahotannin tsaro cewa ‘yan bindiga na amfani da kasuwannin wajen sayar da shanunsu da suka sace.
Sanarwar ta ce, kasuwannin da abin ya shafa sun hada da na Tsafe da Bilbis a karamar hukumar Tsafe da kuma kasuwar Wuya da ke karamar hukumar Anka.
“Sauran sun hada da kasuwar Magamin Diddi a karamar hukumar Maradun, kasuwar Galadi a karamar hukumar Shinkafi, kasuwar Mada da ke karamar hukumar Gusau da Sabon Birnin Danali a karamar hukumar Birnin Magaji.
Sauran kasuwannin su ne; Kasuwar Kokiya, Chigama da Nasarawar Godel, duk a cikin karamar hukumar Birnin Magaji.
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin jihar ta ga ya zama dole ta rufe wadannan kasuwanni saboda rahotannin tsaro cewa ‘yan fashin na hada baki da wasu marasa kishin kasa domin sayar da shanun da suka sace a kasuwannin”.
“Gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda tare da kamo duk wanda ya karya dokar.
“Tun daga nan aka umarci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu a cikin wadannan kasuwannin da abin ya shafa.
Haidar ya yi kira ga al’ummar jihar da su bi wannan umarni tare da ba gwamnatin jihar hadin kai a kokarinta na kawar da ayyukan ‘yan fashi a jihar.


