Gwamnatin jihar Kogi ta ba da umarnin a rufe wata coci a garin Okene, bisa zargin damfarar masu ibada ta hanyar sayar musu da ruwan maganin bindiga.
Haka zalika, an zargi cocin mai suna New Jerusalem Deliverance Ministry da gudanar da wata cibiyar lafiya ba tare da amincewa ba.
Bayanai sun ce fadan coci, Peter Adeiza ya bude cibiyar tun a shekara ta 2008, kuma akwai zarge-zargen cewa mutane da yawa sun mutu saboda haramtattun ayyukan lafiya da rashin tsafta.
Jaridar Punch ta kuma ce an gano baya ga bude asibitin da ake karbar haihuwa da kula da marasa lafiya, ana kuma amfani da cocin a matsayin cibiyar kula da masu tabin hankali, inda aka ga mutane da dama daddaure cikin sarka.