An rantsar da Micheal Usi, wani ɗan wasan barkwanci da ya koma harkar siyasa a matsayin mataimakin shugaban ƙasar Malawi.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a majalisar ƙasar da ke Lilongwe, babban birnin ƙasar.
Usi mai shekara 55, ya maye gurbin Saulos Chilima, wanda ya mutu tare da wasu mutum takwas a farkon watan nan a wani hatsarin jirgin sama.
Mutane sun yi ta sowa da murna lokacin da Dakta Usi yake jawabin bayan shan rantsuwa, inda ya ce ya karɓi matsayin cike da jimami da kuma godiya,
Ya yi alkawarin ɗora wa daga wajen da wanda ya gada ya tsaya, inda ya kuma gode wa shugaban ƙasar Lazarus Chakwera saboda amincewa da shi da mukamin mataimakin shugaban ƙasa.
Naɗin nasa ya raba kan ƴan Malawi da dama.
Wasu dai na ta yaɗa hotunan bidiyonsa a kafafen sada zumunta na wasan barkwanci da yake yi da kuma aza ayar tambaya na cewa ko ya cancanta ya rike irin wannan babban muƙami.