An rantsar da shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, karo na shida a kan karagar mulki.
Shugaban mai shekara 80, ya kasance shugaban kasa mafi dadewa a duniya.
Ya yi alkawarin tafiya da kowa a ƙasar, inda ya ce zai zama shugaba ga kowa. Ya fara hawa kan mulki ne a shekara ta 1979 bayan wani juyin mulki da ya jagoranta.
Masu suka dai sun ce tun bayan lokaci da ya karbi mulki ake ta tafka a magudi a kowane zabe da aka gudanar, inda ake hana ‘yan adawa shiga zabuka da kuma tilastawa kafafen ƴada labarai yin abin da gwamnati da kawayenta ke so. In ji BBC.