An rantsar da Nangolo Mbumba a matsayin sabon shugaban ƙasar Namibiya na huɗu, bayan rasuwar shugaba Hage Geingob da asubahin yau Lahadi.
Mista Mbumba – wanda shi ne mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin mulkin mista Geingob- ya sha rantsuwar kama aikin ne a fadar gwamnatin ƙasar.
An kuma rantsar da Netumbo Nandi_Ndaitwah nan-take, a matsayin mataimakin shugaban ƙasar.
Bayan bikin rantsuwar da aka gudanar cikin jimami da alhini, sabon shugaban ƙasar ya jinjina wa marigayin, wanda ya bayyana a matsayin jagoran tsarin mulki da ya kafa nagartacciyar gwamnati a ƙasar.
A yanzu mista Mbumba zai jagoranci ƙasar har zuwa lokacin da za a gudanar da babban zaɓen ƙasar da za a yi nan da wata tara.