An rantsar da sabon shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe, tare da fatan zai fitar wa kasar kitse daga wuta dangane da matsin tattalin arzikin da take fama da shi.
Sabon shugaban, mai shekara 73 ya sha rantsuwar kama aiki ranar Alhamis a harabar majalisar dokokin kasar cikin tsauraran matakan tsaro.
Ana kallon mista Wickremesinghe, wanda tsohon Firaminista ne, a matsayin wanda ba fitacce ba ga ‘yan kasar, to sai dai wasu masu zanga-zangar sun ce za su ba shi dama.
Kasar Sri Lanka dai ta shafe watanni tana fama da masu zanga-zangar nuna adawa da durkushewar tattalin arzikin kasar.
Inda da yawa ke zargin tsohuwar gwamnatin Rajapaksa da barnatar da kudaden kasar, kuma suke kallon mista Wickremesinghe na da hannu wajen haddasa matsalar. In ji BBC.