Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Falgore, ya rantsar da sabbin mambobin majalisar guda biyu.
Sabbin mambobin, Mohammed Butu-Butu, NNPP-Rimin-Gado/Tofa, da Zakaria Ishak, NNPP-Kura/Garunmalam, sun lashe zaben da aka sake gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu a mazabunsu.
A yayin da yake gabatar da rantsuwar a zaman majalisar, shugaban majalisar ya bukaci sabbin ‘yan majalisar da su yi kokarin ci gaban mazabarsu da ma jihar baki daya.
“A madadin daukacin ’yan majalisa ta tara, ina maraba da sabbin zababbun ‘yan majalisar zuwa zauren majalisar.
Falgore ya ce “Muna yi muku fatan samun karin nasara wajen sauke aikin ku na majalisa.”
Tun da farko hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayar da takardar shedar lashe zaben ga mambobin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP guda biyu da suka doke abokan hamayyar su daga jam’iyyar APC.
Kakakin majalisar ya kuma rantsar da Mohammed Butu-Butu, NNPP-Rimin-Gado a matsayin mataimakin shugaban majalisar, mukamin da ya rike kafin soke zabensa.