Gwamnatin jihar Adamawa ta rantsar da sabbin alkalai takwas da aka nada.
A ranar Juma’a ne babban alkalin jihar, Mai shari’a Nathan Musa ya rantsar da alkalan da aka kara daga kotunan yankin.
A yayin bikin wanda ya gudana a harabar babbar kotun da ke babban birnin jihar, Yola, Mai shari’a Nathan Musa, ya bukaci sabbin alkalai da su yi aiki tukuru bisa ka’idojin da aka gindaya.
Sabbin alkalan kotun guda takwas sun hada da Barista Aliyu Ahmed, Ibrahim Aliyu, Abubakar Habu, Joseph Mafa, Usman Adamu Laido, Bashir Musa, Ibrahim Yusuf da Umar Hamman Audi.
Mai shari’a Nathan Musa ya tunatar da alkalan kotunan kolin shari’a, ya kuma gargade su da su guji nuna son zuciya da rashin sanin yakamata, inda ya kara jaddada aniyar bangaren shari’a na jiha na yin gwagwarmayar tabbatar da adalci da kuma tabbatar da tsafta a bangaren shari’a.
Daya daga cikin sabbin alkalai da aka rantsar, Barista Joseph Mafa wanda ya yi jawabi ga dukkaninsu, ya yabawa babban alkalin da ya same su a matsayin wadanda suka cancanta a matsayin su.


