Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri ya sha rantsuwar kama aiki a wa’adin mulkin jihar na biyu.
An rantsar da gwamnan ne ranar Laraba da rana a baban filin wasa na na Samson Siasia da ke Yenagoa babban birnin jihar.
Gwamna Diri da mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo, sun sha rantsuwar ne a hannun babbar alÆ™aliyar jihar, mai shari’a Matilda Ayemieye.
Hukumar zaÉ“en Najeriya INEC ce ta ayyana Duoye Diri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaÉ“en gwamnan jihar da aka gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata.
Manyan mutane da dama ne suka halarci bikin rantsuwar ciki har da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da tsoffin shugabannin ƙasar, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da matarsa Patience Jonathan, da mataimakin shugaban ƙasar Laberiya Jeremiah Koung.
Daga cikin gwamnonin da suka halarci bikin rantsuwar sun haÉ—ar da gwanonin jihohin Oyo da Plateau da Neja da Osun da Edo da Kwara da kuma Gwamnan Adamawa.