Hukumar zaɓe ta jihar Kano, KANSIEC, ta matso da zaɓen ƙananan hukumomi 44 da ta tsara yi a jihar a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, zuwa ranar 26, ga watan Oktoba, 2024.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai, yau Juma’a a hedikwatar hukumar.
Farfesa Lawan, ya ce sun yi hakan ne domin bin hukuncin Kotun Ƙoli ta Najeriya, da ta bayar da wa’adin zuwa watan Oktoba na tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomi a ƙasar.