fidelitybank

An rage kudin mota da samar da abinci ga talaka a Legas

Date:

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da kafa wuraren bayar da taimakon abinci ga talakawa da sauran masu rauni a cikin al’umma a sassan jihar sakamakon wahalar da aka shiga a dlilin karancin man fetur da takardar kudin kasar ta naira.

Haka kuma gwamnan ya sanar da rage kudin hawa motoci da sauran abubuwan sufuri na haya na gwamnatin jihar da kashi hamsin cikin dari daga yau din nan.

Gwamnan jihar ta Lagos ya kuma bayar da umarni na gaggawa ga dukkanin gidajen mai da ke jihar da su rika sayar da mai ba dare da rana tsawon sa’a domin masu ababen hawa su daina tsayuwa sayen mai tsawon sa’o’i.

Karanta Wannan: NDLEA ta kama hodar Iblis a Legas

A sanarwar da ya fitar ya gargadi bata-gari da sauran miyagu wadanda za su nemi ribatar tsarinwajen haddasa rikici, da cewa duk wanda ya yi kokarin hakan zai gamu da hukunci.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa kalubalen da ke tattare da sauyin kudin ya haddasa matsala ga mazauna birnin na Lagos, inda suka shiga matsi da ya takaita hanyoyin samun kudin da suke hada-hada a kullum wanda hakan ya kuma jefa su cikin wahala.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp