Za a yi wasan zagaye na farko a ranar Alhamis 7 ga watan Afirilu, yayin da za a yi wasan zagaye na biyu a ranar 14 ga watan Afirilu a gasar cin kofin Europa League.
Yayin da za a yi wasan kusa da na karshe a ranar 28 ga watan Afirilu sai wasan zagaye na biyu a ranar 5 ga watan Mayu.
Za dai a gudanar da wasan karshe a ranar Laraba 18 ga watan Mayu a filin wasa na Ramon Sanches-Pizjuan Stadium dake Svilla.
Jerin jaddawalin haduwar da za a kara.
RB Leipzig vs Atalanta
Eintracht Frankfurt vs Barcelona
West Ham vs Lyon
Braga vs Rangers.