Fadar Downing Street ta Birtaniya ta sanar da naɗa tsohon firaministan ƙasar David Cameron a matsayin sakataren harkokin waje na ƙasar.
Mista Cameron ya maye gurbin James Cleverly ne, wanda shi kuma ya maye gurbin Suella Braverman a matsayin sakataren harkokin cikin gida.
A safiyar Litinin ɗin nan aka kori Mrs Braverman daga muƙaminta bayan ta rubuta wata maƙala da ta saɓa wa manufar fadar gwamnatin kan zargin ‘yan sanda da nuna son-kai a zanga-zangar nuna goyon bayan Falasɗinawa